advanced Search
Dubawa
7050
Ranar Isar da Sako: 2019/06/16
Takaitacciyar Tambaya
su wayi shuwagabannin samarin gidan aljanna?
SWALI
Suwa shuwa gabannin matasa nagidan aljanna
Amsa a Dunkule
Imam Hasan da Husain jikokin manzan Allah (saw) shawagabannin ne ga dukkanin ‘yan aljanna kuma su shugabannin samarin gidan aljanna ne. amma shugabancin su ya fi karfi kan samarin da suka yi shadan a lokacin samrtarsu, kuma wannan bai ci karo da shagabancin sauran manzanni da Annabawa a cikin gidan aljanna ba.
A dunkule, bisa la’akari da dalilai wannan na nuna cewa shugabancin wadannan imamai biyu ga dukkanin samarin gidan aljana bai hada har da sauran Annawba da Manzanni ba.
Amsa Dalla-dalla
Manzanni da waliyyai shugabanni ne ga ‘yan digan aljanna kamar yadda Imam Hasan da Husain na daga cikin wadanna shuwagabanni. Gabaki dayan manzanni da waliyyai na da matsayi sama da na sauran yan’gidan aljanna. Amma wani lokaci Allah  ya kan kebanci wasu da wani matsayi na musammani ya ba su wani mukami da zasu kebanta da shi kuma su shahara da shi.
Idan har ana kiran sayyida fadima da “shugaban matan gidan aljanna” kuma ana kiran imami na hudu an yi masa lakabi da “shugaban masu bauta” da “shugaban masu sujjada”, wannan ba ya nifin cewa fadima (as) ba shugaba ce ga maza ba, kuma wannan baya nufin imam sajjad ba shugaba ne ga wadanda ba sa yawaita ibada da sujja ba. Illa iyaka saboda kasantuwar sayyida fatima mace ce da kuma yadda imam sajjad ya zama ya shagaltu da yawan ibada da sujjada a lokacin da makiya suke kewaye da shi suka hana shin ayyukan cigabatar da jama’a da al’umma, sai wannan ya sa ya cancanci wannan lakabi.
Bisa wannan ba za mu iya yin tambaya kamar haka ba mu ce: tun da an yiwa Imam sajjad lakabi da mai ibada da sujjada: kenan ya zama shi ne shugaban masu sujjada baki daya har ma da kakanninsa manzon rahama (saw) da imam Ali kenan? Kuma su ba shuwagabanni ba ne a wannan fagen ba?
Don haka shugabanci Imam Hasan da Husain kan samarin gidan aljannan a bisa irin wannan mahangar ne shi ma, saboda wadannan bayin Allah  a lokcin da musulunci yake farkon zuwa aka haife su kuma kwanakin samartarsu ya hadu da kwanakin samartar musulunci, kuma sun kasance a lokacin da suke samari a lokocin rayuwar manzo da ma bayan samartakarsu a tsakatsakin musulmai ba a sami wasu samari da su ka kai kusa da matsayinsu a fagen takawa da girma ba, don haka suka zama sun cancanci wannan lakabi sai suka zama shuwagannin samari da tsofaffin gidan aljanna.
Domin karfafa wannan bayani da ya gabata zamu kawo muku ruwayoyi guda biyu:
  1. An karbo daga imam sadiK yana cewa ”ku ziyarci kabarin Husain (as) kada ku kaurace masa hakika shi ne shugaban samarin aljanna kuma sugaban samari shahidai.[1]
Bisa la’ajari da wannan ruwayar zamu ga cewa imam Husain ya shahara da wannna lakabi na shugaban shahidai duk da cewa ya yi shahada a lokacin da yake manyanta, lakabin shugaban samari shahidai kuma na nuni bisa kulawar imam ta musamma ga wadanda suka yi shahada a shekarun samarta,  
  1. An karbo daga imam Ali (as) yana cewa manzon Allah  ya ce wani mala’ika ya zo min yana cewa: wani mala’ika ya zo min sannan ya ce da ni ya Muhammad hakika Allah  ta’ala yana cewa da kai: na umarci bishiyar duba da ta dauki durri da yakutu da murjani sannan ta warwatsu kan duk wadanda suka halarci auren fadima na daga mal’iku da hurul ini, kuma lalle sauran mazauna sammai sun yi murna da haka kuma hakika zasu haifi ‘ya’ya biyu shugabanni ni su a duniya kuma da sannu zasu zama shuwagabannin tsofaffi da samarin gidan aljanna kuma hakika za a cika ajanna da ado a sakamakon haka ka yi farinciki ya kai Muhammad hakika kai ne shugaban na farko da na karshe.[2]
A wannan ruwayar ma akwai manuniya kan cewa su shawagabbanin gidan aljanna ne amma la’akari da cewa a cikin aljanna babu tsofaffi kuma ba a tsufa. Don haka a dunkuke zamu iya cewa wadanna jikoki na ma’aiki shuwagababbin ne na dukkanin mutane gidan aljanna kuma amma wannan shugabancin an kalle shi ta bangaren wadanda suke samari suka bar duniya shahidai ko kuma suka rasu, kuma wannan bayanin bai saba da kasantuwar dukkanin ‘yan aljanna samari ne ba, kuma abin da ake nufi da tsofaffin su ne wadanda suka bar duniya bayan sun tsufa.
Wata tambaya da zata iya zuwa kwakwalwa it ace: la’akari da wannan hadisi shin yana nufin Imam Hasan da Husain su shuwgabannin sauran Annabawa da Waliyayyi ne kenan?  Wanda za a iya bada wannan amsa a takaice kamar haka: dukkanin wata Magana tana da togaciya wacce wani lokaci togaciyar ta kan zo a cikin wannan maganar, wani lokaci kuma tagaciyar kan dogara da wani dalili bayyananne, wanda ba bukatar a yi wani dogon bayani kansa.
Bisa wannan asasi abin da za a iya fahimta a nan shi ne shugabancin wadannan imamai biyu kan dukkanin yan aljanna ne, ba kan daidaiku kamar Manzo (saw) imam Ali da sayyida fadima (as) dss ba.....
Zamu iyan karfafa wanna maganar da ruwayar nan mai zuwa wacce ta yi kama da abin da muke Magana a kai.
Wani mutun ya tambayi imam sadik cewa shin da gaske ne mazon Allah (saw) ya ce Abuzarri ne mafi gaskiyar mutane sai imam sadik ya ce masa haka ne, sai ya ce to ina manazun Allah da imam Ali suke?  sannan ina Imam Hasan da Husain? Shin wannan yana nifin Abuzarri ya fi su fadar gaskiya? Bayan da imam ya yi wasu bayanai sannan sai ya ce mu Ahlubaiti ba a sawa da mu cikin irin wannan kiya sin.[3]
Wannan na nifin bisa la’akari da dalilai da abubuwa na sarari zaka iya fahimtar cewa fadin gaskiyar Abuzarri an kwatanta shi ne da sauran mutane ba da Ahlulbaiti (as) ba, duk da cewa babu wannnan bayain dalla-dalla a cikin ruwaya.
 

[1] Sawabul a’amal na shekh saduk shafi 97.
[2] Sahifar ridha (as) shafi 94
[3] Ma’anil akhbar na shekh sadukj1 shafi 179
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

  • ina aka samo asalin madogarar gabatuwar jagorancin malami
    8281 Tsare-tsare 2012/07/24
    Mas'alar jagorancin malami a matsayin shugaban al'umma a musulunci wani hakki ne da aka sanya shi ga wanda ya kai matakin ijtihadi. Wasu suna ganin lamari ne sabo a cikin fikirar musulunci, sai dai jagorancin malami a matsayin wani umarni na mai shari'a mai tsarki a lokacin ...
  • shin Imamul hujja a tsibirin bamuda yake zaune?
    14911 تاريخ بزرگان 2012/07/25
    Dalilin da ya sa wasu mutane suka yi ammanar cewa “Tsibirin Bamuda shi ne mazaunar Imamu Mahdi (a.s), gani suke Tsibirin Bamuda shi ne “Jazijrayul Khadra’a”. Bisa kaddara cewa Jaziratuk Khadra’a ita ce mazaunar Imamu Mahdi (a.s) shi ya sa suka ce Tsibirin Bamuda ya kunshi wadannan ...
  • Menene hukunchi namijin da ba ya iya biyawa matarsa hakkokinta?
    12493 2019/06/16
    dawwamar rayuwar aure da karfafarta ya dogara da soyayya da kauna da fuskantar juna da girmama juna. Domin iyali su samu tsayuwa da dawwama Addini Muslunci ya sanya hakkoki ga kowanne dayansu ya kuma ayyana musu wajibai a kansu, duk sa”ilin da aka ce akwai hakkoki to ...
  • menene dalili a kan tabbatar shugabancin malami.
    17279 Hakoki da Hukuncin Shari'a 2012/07/26
    Akwai hanyoyi mabanbanta domin tabbatar da “shugabancin malami” sai dai a nan za mu isu da ambaton dalilai guda biyu na hankali da na ruwaya domin tabbatar da ita. Dalili na hankali: Hankali ya tabbatar da wajabcin samun mutumin da ke ...
  • Shin namiji na da wani fifiko a kan mace ta bangaren halitta?
    7667 Falsafar Musulunci 2017/05/21
    Da namiji da mace sun ginu ne a kan abu guda kuma sun samo asali daga tushe guda da kuma rai guda. Sai dai alakarsu da juna shine kan kai su zuwa ga kamala saboda haka ba wani hanya ma da za a iya kwatantasu a matsayin ...
  • mece ce alakar jagorancin malami da jam'iyyu?
    6470 Tsare-tsare 2012/07/24
    Kungiyoyin siyasa, da ma'anar wasu jam'iyyu masu iri-iri akwai su a cikin kowace al'umma tun zamanin da. A yanzu ana ganin jam'iyyun siyasa a matsayin wani abu na tarayyar mutane da 'yancin zabe ne. bisa wannan asasin ne ya zama dole mu kalli wannan lamari a matsayin ...
  • Menene Hukuncin musulmin da ya kashe kafirin da ba bazimme ba?
    6062 حدود، قصاص و دیات 2017/05/22
    Hukuncin musulumci kan kisa idan na gangan ne kisasi za a yi (Kisasi shi ne kashe wanda ya yi kisan kai) idan kuma ba na gangan ba ne diyya za abiya. Amma kafin a yiwa wanda ya yi kisan kai Kisasi akwai sharaDai da ya zama idan ...
  • mi ake nufi da makamta a ranar lahira?
    14494 Tafsiri 2012/11/21
    Abun nufi da makamta a cikin wannan ayar[i] da sauran ayoyi makamantanta[ii] ba shi ne rashin gani irin na duniya ba {wato mutun ya zamo bai gani da idanuwan da yake dasu} , sai dai abun nufi shi ne mutun da ...
  • Shin Dukkan Hadisan Da Suka Zo Game Da Mas’alar Auren Mutu’a Karbabbu Ne?
    15766 Dirayar Hadisi 2012/07/24
    Aure Mai Tsayayyen Lokaci Sunna ne daga Cikin Sunnonin Musulunci, Wanda Halaccinsa ya zo A Cikin Alkur’ani Mai Girma, Kuma Wannan Sunnar ta Gudana A Lokacin Manzon Allah Mafi Girma (s.a.w) da Lokacin Halifa na Daya, da Wani Sashi na Lokacin Halifa na Biyu, Har Lokacin da ...
  • mene ne dalilin haramcin marenan raguna?
    8146 Hikimar Hakkoki da Hukuncin Shari'a 2012/07/25
    Allah madaukaki mai hikima ne, kuma mai hikima ba ya yin wani aiki da wasa da babu hikima, saboda haka ne duk shi’a suka yi imani da cewa dukkan hukunce-hukunce suna kasancewa bisa maslaha ne, kuam a wasu wuraren an yi nuni da dalilin haramci a wasu ...

Mafi Dubawa