advanced Search
Dubawa
82673
Ranar Isar da Sako: 2019/06/16
Takaitacciyar Tambaya
Illolin wasa da azzakari, manyan zunubai, wankan janaba, dalilan haramci
SWALI
menene hukuncin wanda ke yin wasa da azzakarinsa har ya kai gafitar da maniyyi?
Amsa a Dunkule
Ya kamata mu san cewa wannan aiki na wasa da azzakari haramun ne a mahangar muslunci sannan dukkanin mai aikata wannan aiki ya na cikin masu aikata manyan zunubai.[1]  [2]
Istimna”I {wasa da azzakari} kala-kala ne kamar misalin wasa da azzakari da hannu da kuma misalin sauraren muryar macen da ba muharrama ba, ko kuma yin musayen kalaman soyayya, da yin tunanin abubuwada masu matso sha”awa.
Dukkanin wanda ya yi amfani da daya daga cikin wadannan abubuwa da muka ambata suka kai shi ga fitar da maniyyi to wannan aikin nasa sunansa istimna”I wanda yake haram ne.[3]
Wajibi ne wanda yake aikata wannan mummunar dabi”a ya tuba ya kuma yi wankan janaba don cika sharuddan ibada, tabbas dukkanin wanda ya daura damarar kuma ya yi aniyar tuba da barin wannan mummunan aiki ya kuma nemi taimakon ubangiji a kai to ubangiji zai taimaka masa.[4]
Ya zo a Cikin hadisai masu tarin yawa cewa an yi hani kan wannan mummunar dabi”a ta istimna”i.
Manzon Allah {s.a.w} yana cewa: dukkanin wanda yake auren tafin hannunsa {wasa da azzakari} ya nesanta da ga rahamar ubangiji.
Abu basir yana cewa na ji daga imam sadik {as} yana cewa: ubangiji ba zai Magana da nau”o’in mutane uku ba kuma ba zai kale su ba, kuma ba zasu tsarkaka daga zunubai ba kuma azaba mai radadi na jiransu. Daya daga cikin wadanna gungun sune wadanda suka kasance suna aurar tafin hannunsu wato suna (wasa da zakarinsu har sai maniyyi ya fita).
An tambayi imam sadik kan mummunar al’ada ta boye (wasa da zakari), yayin da yake ba da amsa sai ya ce: babban zunubi ne kuma wanda Allah madaukaki yayi hani da shi a cikin littafinsa mai tsarki kuma wanda yake yin wannan aikin tamkar wanda ya auri kansa ne kuma idan har na san wani yana aikata haka ba zan ci abinci tare da shi ba. Sai mai tambaya ya ce: ya dan manzon Allah (saw) yi mana bayanin hanin Allah a cikin littafinsa: sai ya ce wanda yake neman biyan bukatarsa {ba ta hanyar da Allah ya halatta ba} to azzalumi ne shi.
Bari mu kawo muku wasu wasu shashi ne daga ruwayoyin da ke yin nuna kan tsananin kin Allah ga wannnan aiki da kuma haramcinsa.[5]
Daya daga cikn dalailan da suka sa musulumci ya haramta wannan aiki shi ne, irin cututtuka msau yawa da yake jawo wa jika da ruhi da hankali kuma a yau ci gaban ilimi ya gano wasu daga cikinsu. Kuma mai yiyuwa nan gaba a karo gano wasu illolin na daban.[6] A yau an gano illolin da wasa da zakari ke haifarwa wadannan zamu iya kasa su zuwa kaso biyu:
 
Na daya: cututuka na ruhi.
  1. Wannan zunbuni na nesanta mutum daga Allah ta yadda a ranar lahira Allah ta’ala ko kallon masu wannan laifi ba zai yi ba kuma ba zai yi Magana da su ba kuma yana hana su samun wasu abubuwa mihimmai kamar tsarkakakken ruhi da nisantar abubuwan da aka haramta dss.
  2. A sakamakon bin tauyayayyar hanyar biyna bukata wacce ba ta dabi’a ba, bayan da mai wannan dabi’a ya yi aure mafi yawa ba sa iya zama da matansu kamar yadda ya kamata zaka same shi rarrauna wajen biyna bukatar matarsa ta kwanciya, kari a kan matsaloli na zamantakewar yau na gobe, daga karshe hakan ya kai ga tarwatsewar rayuwarsu ta aure.
  3. Mutuwar jiki da rashin damuwa da abubuwa mihimmai na rayuwa, yawan damuwa da kunci da ma wasu illoli da suka shafi ruhi.
  4. Yana jawo dakushewar tunani da daidaitar tunani da raunin harda da raunanan himma.
  5. Yawaita sanyin jiki da rudewa dss.
  6. Saurin gajiya da raunanar jijiyoyin da ke karfafa ruhi.
  7. Saurin jin gajiya daga karamar wahala da daukar zafi a mafi karancin taho mu gama da wasu.
Na buyu: cututtuka na jiki:
  1. Wannan ya jarrabtu da wannan dabi’ar yana fama da matsaloli na ruhi da jiki kuma a sannu a sannu sai ya wayi gari rarrauna, wanda ba ya iya komai, wanda bai san ciwon kansa ba, mai debe tsammani. da ga karshe sai ya zama wanda hankalinsa ya tabu kuma ya rika yi wa wasu mummunan kallo.
  2. Yawaita motsa al’aurarsa da wuce iyaka da bawa gabbai saduwa aikin tukuru na jawo saurin girma da tsufa.
  3. Yawan maimata wannan aiki na jwo gaba dayan jiki  ya yi rauni daga karshe nan da nan sai ya tsofe.
  4. Saboda yawan gudanar jinni a cikin gabbai masu haihuwa, kwakwakwarsa da sauran gabbai na samun rauni wajen iya gudanar da jinni kamar yadda ya kamata.
  5. Yawan tayar da jijiyoyi da rashin gamsuwa a lokaci mai tsawo na sa jijiyoyi su yi rauni kuma hakan na taba ruhin mutum.
  6. Raunana gani da rashin jin dandano da raunin kashi da ciwon gabbai.
  7. Kamuwa da cutar karancin jini, musamman ma sakamakon yawaita motsa zakari a koda yaushe.  
  8. Lalacewar ma’ajiyar maniyyi.
  9. Lalacewar babgaren karkashin ma’ajira maniyyi da kuma gabansa.
  10. Lalacewa gabban haihuwa kamar rashin iya rike maniyyi da kuma rashi iya rike fitsari.
Abin lura a nan shi ne duk da cewa an yi bayanin illolin da istim’na’I yake haifarwa, sai dai ba za mu iya cewa dalilin da ya sa aka haramta shi su ne wadanda muka ambata a nan kadai ba.[7] Ballantana ma zai iya yiyuwa suna da wasu illolin na jiki da na ruhi na daban wadanda har yanzu ba mu san su ba, don haka muna da tabbacin cewa hukunce-hukuncen da suke daga Allah ta’ala baki dayansu sun doru ne kan mas’laha da barna.                         
 
 

[1] An sanya wannan laifi daga cikin jerin zina kamar yadda ya zo a ruwaya cikin wasa;ilu shi’a j20 shafi 352.
[2] A dakko daga tambaya ta 326.  
[3] Mujma”ulrasa”il muhashsha shafi 34 da manasik na imam khomaini shafi 163 da shafi 334.
[4] Don samun bayani sosai kan hanyoyin barin isimna’I a koma tambaya ta 2294.
[5] An ciro daga tambaya ta 1262.  
[6] An ciro daga tambaya ta 1575.
[7] An ciro daga tanbaya ta 1744.  
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

  • ina aka samo asalin madogarar gabatuwar jagorancin malami
    8281 Tsare-tsare 2012/07/24
    Mas'alar jagorancin malami a matsayin shugaban al'umma a musulunci wani hakki ne da aka sanya shi ga wanda ya kai matakin ijtihadi. Wasu suna ganin lamari ne sabo a cikin fikirar musulunci, sai dai jagorancin malami a matsayin wani umarni na mai shari'a mai tsarki a lokacin ...
  • shin Imamul hujja a tsibirin bamuda yake zaune?
    14911 تاريخ بزرگان 2012/07/25
    Dalilin da ya sa wasu mutane suka yi ammanar cewa “Tsibirin Bamuda shi ne mazaunar Imamu Mahdi (a.s), gani suke Tsibirin Bamuda shi ne “Jazijrayul Khadra’a”. Bisa kaddara cewa Jaziratuk Khadra’a ita ce mazaunar Imamu Mahdi (a.s) shi ya sa suka ce Tsibirin Bamuda ya kunshi wadannan ...
  • Menene hukunchi namijin da ba ya iya biyawa matarsa hakkokinta?
    12493 2019/06/16
    dawwamar rayuwar aure da karfafarta ya dogara da soyayya da kauna da fuskantar juna da girmama juna. Domin iyali su samu tsayuwa da dawwama Addini Muslunci ya sanya hakkoki ga kowanne dayansu ya kuma ayyana musu wajibai a kansu, duk sa”ilin da aka ce akwai hakkoki to ...
  • menene dalili a kan tabbatar shugabancin malami.
    17279 Hakoki da Hukuncin Shari'a 2012/07/26
    Akwai hanyoyi mabanbanta domin tabbatar da “shugabancin malami” sai dai a nan za mu isu da ambaton dalilai guda biyu na hankali da na ruwaya domin tabbatar da ita. Dalili na hankali: Hankali ya tabbatar da wajabcin samun mutumin da ke ...
  • Shin namiji na da wani fifiko a kan mace ta bangaren halitta?
    7667 Falsafar Musulunci 2017/05/21
    Da namiji da mace sun ginu ne a kan abu guda kuma sun samo asali daga tushe guda da kuma rai guda. Sai dai alakarsu da juna shine kan kai su zuwa ga kamala saboda haka ba wani hanya ma da za a iya kwatantasu a matsayin ...
  • mece ce alakar jagorancin malami da jam'iyyu?
    6470 Tsare-tsare 2012/07/24
    Kungiyoyin siyasa, da ma'anar wasu jam'iyyu masu iri-iri akwai su a cikin kowace al'umma tun zamanin da. A yanzu ana ganin jam'iyyun siyasa a matsayin wani abu na tarayyar mutane da 'yancin zabe ne. bisa wannan asasin ne ya zama dole mu kalli wannan lamari a matsayin ...
  • Menene Hukuncin musulmin da ya kashe kafirin da ba bazimme ba?
    6062 حدود، قصاص و دیات 2017/05/22
    Hukuncin musulumci kan kisa idan na gangan ne kisasi za a yi (Kisasi shi ne kashe wanda ya yi kisan kai) idan kuma ba na gangan ba ne diyya za abiya. Amma kafin a yiwa wanda ya yi kisan kai Kisasi akwai sharaDai da ya zama idan ...
  • mi ake nufi da makamta a ranar lahira?
    14494 Tafsiri 2012/11/21
    Abun nufi da makamta a cikin wannan ayar[i] da sauran ayoyi makamantanta[ii] ba shi ne rashin gani irin na duniya ba {wato mutun ya zamo bai gani da idanuwan da yake dasu} , sai dai abun nufi shi ne mutun da ...
  • Shin Dukkan Hadisan Da Suka Zo Game Da Mas’alar Auren Mutu’a Karbabbu Ne?
    15766 Dirayar Hadisi 2012/07/24
    Aure Mai Tsayayyen Lokaci Sunna ne daga Cikin Sunnonin Musulunci, Wanda Halaccinsa ya zo A Cikin Alkur’ani Mai Girma, Kuma Wannan Sunnar ta Gudana A Lokacin Manzon Allah Mafi Girma (s.a.w) da Lokacin Halifa na Daya, da Wani Sashi na Lokacin Halifa na Biyu, Har Lokacin da ...
  • mene ne dalilin haramcin marenan raguna?
    8146 Hikimar Hakkoki da Hukuncin Shari'a 2012/07/25
    Allah madaukaki mai hikima ne, kuma mai hikima ba ya yin wani aiki da wasa da babu hikima, saboda haka ne duk shi’a suka yi imani da cewa dukkan hukunce-hukunce suna kasancewa bisa maslaha ne, kuam a wasu wuraren an yi nuni da dalilin haramci a wasu ...

Mafi Dubawa