Idan muka lura da ayoyi da ruwayoyi da suka zo za mu fahimci cewa Allah madaukaki bayan siffofi na mai rahama mai jinkai {rahmanin rahim} alokaci daya kuma ya na da siffofi na tsanani da fushi; ma'ana shi mai gafarta zunubi ne, kuma mai tsanani azaba ne.
Idan muka yi duba a nutse, a kan irin lokutan da wadancan Imamai guda biyu (a.s) suka yi rayuwar su, za a fahimci dalilin da zai sa zai yi wuya a samu daman rubuta hadisansu cikin wani littafi na musamman. Amma dai wannan baya nufin cewa al’amarin ...
Majalissar kwararru ta zaben shugaba ta hada fakihai {wato masana a cikin fikhu} a cikin dokokin tsarin mulkin na jamhuriyyar musulunci ta iran a bisa doka ta 107, ya tanadi zabe wanda a keyi duk bayan shaikara takwas {8}domin zabar shugaba da kuma lura da yanda yake ...
A cikin koyarwar musulunci, mata suna da matsayi na musamman, ruwawoyi na manzon Allah da a imam[a. s] sun yi bayanin a kan hakan. Ya zo a cikin ruwayoyin mu cewa mata salihai tushe ne na alkhairi da albarka kuma suna cikin abubuwa masu daraja da kima ...
A mahangar Shi'a, jagorancin malami a lokacin boyuwar Imam Mahadi (a.s), shi ci gaba ne na jagorancin imamai ma'asumai (a.s), kamar yadda su ma jagorancinsu ci gaba ne na jagorancin manzon Allah (s.a.w). ...
A kan sami ra’ayoyi guda biyu a kan maganar auren ‘ya’yan Adam (amincin Allah ya tabbata a gare shi). A wannan zamanin ba a sanya dokar haramcin dan’uwa ya auri ’yar’uwarsa ba, kuma ba wata hanyar kiyaye tsatso na mutane domin idan ba ta wannan ...
Halaccin takalidi na daga cikin lamuran da ke wajabta wa mai yin takalidi ya yi iya kokarinsa a cikin lamarin kuma lalle fatawar mujtahidi ba ta isar wa mai yin takalidi, saboda haka wannan mas’alar na daga cikin mas’ala mafi girman mihimmanci. Sananne ne cewa ...
Ma’anar tayarwa a luga da kuma a ma’ana ta shari’a: A ma’ana ta luga taro yana nufin a tattara abu waje daya, amma a yaren shari’a, yana nufin Allah zai tattara halittu domin ya yi musu tambaya su ba da amsa. Hakika an zo da ra’ayoyi guda ...
Ta fuskacin yadda Kur’ani yake gajiyar da mutane ba zai taba yiwuwa a ce ba littafin Allah ba ne, domin gajiyarwar tasa ba a wannann zamanin ba ne kawai har ma a kowane zamani, kamar gajiyarwar da ya yi wa masana balaga ba ta kebanta da wani ...
Ya kamata mu san cewa wannan aiki na wasa da azzakari haramun ne a mahangar muslunci sannan dukkanin mai aikata wannan aiki ya na cikin masu aikata manyan zunubai.[1] [2] Istimna”I {wasa da azzakari} kala-kala ne kamar misalin wasa da azzakari ...
Daga tarin ayoyi da ruwayoyi da kuma tafsire zamu iya anfana da cewa a cikin lamarin kisan kai da annabi halliru ya aikata wato kashe yaro matashi, ba ya aikata hakan bane domin son rai da fushi ba, sai dai dan yana da tabbacin cewa a cikin ...
kafin mu Amsa wannan tambayar yana da kyau a san cewa, su ruwayoyi gaba dayansu, za a iya kasa su kashi biyu, kashi na farko, anace musu ingantattu masu karfi… Akwai kuma wani kashin na ruwayoyi, wadanda ake ce musu raunana, wadanda ba za a iya jingina ...
Abdulqadir Jilani da ake yi wa laqabi da gausul a’azam shi masani ne sufi da aka haife shi a arewacin iran a qarni na biyar, wanda ya mutu a bagdad a qarni na shida. Amma alaqarsa da imam Sadiq (a.s) da savawarsa gare shi to ...
Duk da yake Annabin Musulunci wanda shi ya fi girma, shi ne mafificin Annabawa, kuma mafi daukakar daraja, to amma wannan Hususiyar tasa (wato girman da ya kebantu da ita) bai zamo wajibi ya zamo dole sai ya tattaro dukkan kebance-kebancen dukkan Annabawa da Manzanni ba, a ...
Mafarki wani al’amari ne dake faruwa ga dukkan mutane (a cikin barcinsu) a tsawon rayuwarsu. Sai dai har yanzu malamai ba su iya samun cikakkiyar saninsa ba da yadda yake faruwa. Al’kar’ani mai girma ya bamu labarin Annabi Yusuf (a.s) game da mafarkinsa na gaskiya
Sabo kamar wani jiki ne mai wari da duk sa'dda aka nutse cikin yin sa to sai mutum ya rika jin warinsa ya ragu sakamakon ya zama jikinsa, domin zai daina jin warinsa daga karshe ya dulmuye cikinsa sosai. Kuma idan mutum ya yi azamar komawa daga ...
Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
Kur'ani mai girma ya tabbatar da samuwar aljani kuma ga wasu daga cikin bayanai kan aljani. 1- Aljani halittace da aka yi shi da wuta saBanin mutum shi da kasa aka halicce shi.[1] 2- Yana da ilimi da idraki da tantance Karya daga gaskiya, ...
Lalle Alkura'ani ma ya tabbatar da akwai maita, inda ya nuna wasu alamu da suke gaskata abin da tarihi ya tabbatar na daga cikin abin da Al’kur'anin ya zo da shi na daga al’umman da suka shude. Wasu malamai a wannan zamanin suna ganin wasu daga cikin ...