advanced Search
Dubawa
33940
Ranar Isar da Sako: 2017/05/22
Takaitacciyar Tambaya
Shin zai yiyu a sami alaKa tsakanin Mutum da Aljani?.
SWALI
Shin zai yiyu Dan’adam ya yi akaKa da aljani? Idan har zai yiyu, ya hukuncin yin haka yake?
Amsa a Dunkule
Kur'ani mai girma ya tabbatar da samuwar aljani kuma ga wasu daga cikin bayanai kan aljani.
1-            Aljani halittace da aka yi shi da wuta saBanin mutum shi da kasa aka halicce shi.[1]
2-            Yana da ilimi da idraki da tantance Karya daga gaskiya, yana iya yin magana kuma yana kafa dalili.[2]
3-            An wajabta masa ayyuka (na ibada da dss) da kuma nauyaye nauyaye.[3]
4-            Wasu daga cikin su muminai ne salihai wasu kuma kafirai.[4]
5-            Za a tashe su ranar alkiyama kuwa za a yi musu hisabi.[5]
6-            Suna iya keta sararin samaniya su sato ji amma daga baya an hana su.[6]
7-             Suna kulla alaka da wasu daga cikin mutane kuma suna yin amfani da masaniyar da suke da ita na wasu Boyayyaun sirrika su halakar da mutane.[7]
8-            A cikin su akwai waDanda suke da karfin da iko na gaske kamar yadda ake samu a cikin mutane.[8]
9-             Suna da ikon yin wasu ayyuka da mutane ke bukatuwa zuwa gare su[9].
10-          Su aka fara halitta a doron kasa kafin ahalicci mutane[10].
11-          A cikin Kissar Annabi sulaiman (as) lokacin da Ifritu daga cikin aljanu ya yi da’awar cewa zai iya kawo gadon BilKisu wajen Annabi Sulaiman (as) kafin ya tashi daga mazauninsa[11], Annabi Sulaiman (as) bai Karyata shi ba duk da cewa wannan maganar ba ta zo a cikin Kur'ani ba cewa ya kawo gadon ba[12]
Daga cikin abin da aka amabata a cikin yoyiyn da muka kawo zamu fahimci cewa aljanni ba halitta ce irin ta tatsuniya da labara ba, shi halitta ne samamme a haKiKa, mai jiki wanda za a iya yin alaKa da shi, kuma wasu daga cikin mutane sun yi alaKa da shi, duk da cewa a zamanin da an fadi wasu nau’o’i na alaka daban daban tsakanin mutane da aljani, amma mu zamu takaitu da irin wacce muka samu a cikin Kur'ani da hadisi, da ita zamu isu don wannan kawai muka yarda da shi.
A nan za mu yi nuni zuwa ga yanayin alaKar da muka samu a cikin Kur'ani da ruwayoyi da kuma maganganun da aka naKalto daga wasu maKiya:
A.            Neman tsarin Allah daga aljanai; ya zo a Kur'ani mai girma cewa: {haKiKa wasu mazaje daga mutane sun kasance suna neman tsari wajen wasu mazaje daga aljanu sai suka kara jefa su cikin bala’i da “wahala”}[13].
Al’adar larabawa ta kasance duk lokacin da suka shiga daji mai ban tsoro (misali mai duhuwa) suna neman tsari daga aljanun wannan kwazazzabon, kuma musulunci bai hana yin haka ba kuma ya yi umarni da a nemi tsari daga shaiDanun mutane da na aljan[14].
B.             Tasarrufi da aljani; yin tasarrufi da aljani da yin amfani da su wajen yin hidima duk da cewa abu ne mai yiyuwa, sai dai malamai sun yi bahasi kan cewa shi ya halatta ko kuwa? Gwargwadon abin da suka yarda da shi, shi ne lalle ne kar wannan aikin ya zama ta hanyar da shari’a ta haramta, ko kuma ya zama sanadin cutuwar aljanu. Kuma lalle ne ya zama aikin da suke yi ba wanda shari’a ta haramta ba ne. kuma lalle yin aikin da shari’a ba ta yarda da shi ba ya haramta daidai ne da wasiDa ko babu wasiDa.[15]
An tambayi Marja’I Mai girma Sayyid Ali (as) Khamna’i kan hukuncin zuwa wajen mutanen da ke tasarrufi da rauhanai da aljanu wajen yi wa mutane magani tare da la’akari da cewa bisa  yaKini su aikin alkhairi kawai suke yi, sai ya bada amsa da cewa: wannan aikin ba shi da mushkila a kan kansa da sharaDin cewa ya zama yana yin aiki ta hanyar da shari’a ta halatta[16].
Domin samun Karin bayani a komawa jigogi masu zuwa:-
1.             Abin da sheDan a aljani suke iya yi, tambaya ta 883.
2.             SheDan mala’ika ne ko aljani? Tambaya ta 857.
3.             Littafin aljani da sheDan na Ali Ridha, Tehrani. wanda aka yi tahKiKinsa a mahanga ta Kur’ni da ruwaya da hankali da ilimin rijalu (mazajen hadisi). 
 

[1] Surar rahaman aya 15.
[2] Ayoyi mabanbanta a cikin surar Jinni.
[3] Ayoyi mabanbanta a cikin surar Jinni da Rahaman.
[4] Ayoyi mabanbanta a cikin surar Jinni da Rahaman.
[5] Adreshin da ya gabata 15.
[6] Adreshin da ya gabata 9.
[7] Adreshin da ya gabata 6.
[8] Surar Namli aya 39.
[9] Surar Saba’i aya ta 12 da 13.
[10] Surar Hijiri aya ta 27.
[11] Surar Tururuwa aya ta 30 – 40.
[12] Jawadi Amuli Abdullah a cikin tafsirul maudhu’I j1 shafi 119.
[13] Surar Jinni aya ta 6.
[14] Biharul Anwar j 92 shafi 148 (almahasin) Manzo (saw) ya ce: “Idan masihirtan aljanu su ka motsa, ku kare sharrinsu da kiran salla”.
[15] Mihajus Salihin na sayyid khu’I j 2 shafi na 8.
[16] Taudhihul  masa’il (mai hashiya na Imam khomaini) j 2 shafi 980, 1232.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

  • ina aka samo asalin madogarar gabatuwar jagorancin malami
    8281 Tsare-tsare 2012/07/24
    Mas'alar jagorancin malami a matsayin shugaban al'umma a musulunci wani hakki ne da aka sanya shi ga wanda ya kai matakin ijtihadi. Wasu suna ganin lamari ne sabo a cikin fikirar musulunci, sai dai jagorancin malami a matsayin wani umarni na mai shari'a mai tsarki a lokacin ...
  • shin Imamul hujja a tsibirin bamuda yake zaune?
    14911 تاريخ بزرگان 2012/07/25
    Dalilin da ya sa wasu mutane suka yi ammanar cewa “Tsibirin Bamuda shi ne mazaunar Imamu Mahdi (a.s), gani suke Tsibirin Bamuda shi ne “Jazijrayul Khadra’a”. Bisa kaddara cewa Jaziratuk Khadra’a ita ce mazaunar Imamu Mahdi (a.s) shi ya sa suka ce Tsibirin Bamuda ya kunshi wadannan ...
  • Menene hukunchi namijin da ba ya iya biyawa matarsa hakkokinta?
    12493 2019/06/16
    dawwamar rayuwar aure da karfafarta ya dogara da soyayya da kauna da fuskantar juna da girmama juna. Domin iyali su samu tsayuwa da dawwama Addini Muslunci ya sanya hakkoki ga kowanne dayansu ya kuma ayyana musu wajibai a kansu, duk sa”ilin da aka ce akwai hakkoki to ...
  • menene dalili a kan tabbatar shugabancin malami.
    17279 Hakoki da Hukuncin Shari'a 2012/07/26
    Akwai hanyoyi mabanbanta domin tabbatar da “shugabancin malami” sai dai a nan za mu isu da ambaton dalilai guda biyu na hankali da na ruwaya domin tabbatar da ita. Dalili na hankali: Hankali ya tabbatar da wajabcin samun mutumin da ke ...
  • Shin namiji na da wani fifiko a kan mace ta bangaren halitta?
    7667 Falsafar Musulunci 2017/05/21
    Da namiji da mace sun ginu ne a kan abu guda kuma sun samo asali daga tushe guda da kuma rai guda. Sai dai alakarsu da juna shine kan kai su zuwa ga kamala saboda haka ba wani hanya ma da za a iya kwatantasu a matsayin ...
  • mece ce alakar jagorancin malami da jam'iyyu?
    6470 Tsare-tsare 2012/07/24
    Kungiyoyin siyasa, da ma'anar wasu jam'iyyu masu iri-iri akwai su a cikin kowace al'umma tun zamanin da. A yanzu ana ganin jam'iyyun siyasa a matsayin wani abu na tarayyar mutane da 'yancin zabe ne. bisa wannan asasin ne ya zama dole mu kalli wannan lamari a matsayin ...
  • Menene Hukuncin musulmin da ya kashe kafirin da ba bazimme ba?
    6062 حدود، قصاص و دیات 2017/05/22
    Hukuncin musulumci kan kisa idan na gangan ne kisasi za a yi (Kisasi shi ne kashe wanda ya yi kisan kai) idan kuma ba na gangan ba ne diyya za abiya. Amma kafin a yiwa wanda ya yi kisan kai Kisasi akwai sharaDai da ya zama idan ...
  • mi ake nufi da makamta a ranar lahira?
    14494 Tafsiri 2012/11/21
    Abun nufi da makamta a cikin wannan ayar[i] da sauran ayoyi makamantanta[ii] ba shi ne rashin gani irin na duniya ba {wato mutun ya zamo bai gani da idanuwan da yake dasu} , sai dai abun nufi shi ne mutun da ...
  • Shin Dukkan Hadisan Da Suka Zo Game Da Mas’alar Auren Mutu’a Karbabbu Ne?
    15766 Dirayar Hadisi 2012/07/24
    Aure Mai Tsayayyen Lokaci Sunna ne daga Cikin Sunnonin Musulunci, Wanda Halaccinsa ya zo A Cikin Alkur’ani Mai Girma, Kuma Wannan Sunnar ta Gudana A Lokacin Manzon Allah Mafi Girma (s.a.w) da Lokacin Halifa na Daya, da Wani Sashi na Lokacin Halifa na Biyu, Har Lokacin da ...
  • mene ne dalilin haramcin marenan raguna?
    8146 Hikimar Hakkoki da Hukuncin Shari'a 2012/07/25
    Allah madaukaki mai hikima ne, kuma mai hikima ba ya yin wani aiki da wasa da babu hikima, saboda haka ne duk shi’a suka yi imani da cewa dukkan hukunce-hukunce suna kasancewa bisa maslaha ne, kuam a wasu wuraren an yi nuni da dalilin haramci a wasu ...

Mafi Dubawa