advanced Search
Dubawa
42402
Ranar Isar da Sako: 2012/03/15
Takaitacciyar Tambaya
Ta yaya Mutum zai iya samun ikon fassara Mafarki?
SWALI
Ta yaya Mutum zai iya samun ikon fassara Mafarki? Shin ko akwai Hadisi a kan haka?
Amsa a Dunkule

Mafarki wani al’amari ne dake faruwa ga dukkan mutane (a cikin barcinsu) a tsawon rayuwarsu. Sai dai har yanzu malamai ba su iya samun cikakkiyar saninsa ba da yadda yake faruwa.

Al’kar’ani mai girma ya bamu labarin Annabi Yusuf (a.s) game da mafarkinsa na gaskiya[1], kuma Allah ya hore masa fassara mafarki[2]. Kamar yadda ya fassara mafarkin abokan zamansa na kurkuku, da mafarkin Sarkin Misra, a wajen kurkuku ke nan dai fassarar mafarki, ko tawilin mafarki[3], a bisa irin kalmomin sunaye na Alkar’ani, shi al’amarine tabbatacce, na hakika, kuma wannan din wani ilimi ne wanda Allah ya sanar da wannan annabin, Annabi Daniyal yana daga cikin wadanda Allah ya ba su ilimin fassara mafarki[4]. Kuma hakika Kur’ani ya ambaci wasu shaidu na wasu Annabawan da Allah ya karfafa da gaskanta ingancin mafarkansu[5].

Game da rarraba ruwayoyi na nau’in mafarki, za mu ga kaso biyu na abubuwa da ake gani a cikin barci.

Wasu abubuwn da ake gani a cikin barci mafarkine na gaskiya, wasunsu kuma na karya ne[6]. ruwayoyi sun ambaci cewa; “Hakika mafarki na gaskiya wani yanki ne daga cikin yankin Saba’in na Annabaci”[7] shi irin wannan ilimin ba ana samunsa ne ta hanyar koyarwa da koyo ba, sai dai yana bukatar tazkiya da tsarkake rai, a saboda haka ne babu masu samun irin wannan baiwar sai yan mutane kadan kawai.

A cikin wasu littattafai na fassarara mafarki an ambaci wasu asasi da ka’idoji, sai dai ya wajaba mu lura da cewa wadannan asasin da ka’idojin, ba su ne komi da komi ba, kuma ba na gama gari ba ne, domin suna canzawa, a saboda bambaci su masu yin mafarkin, da wasu sharudda na daban. A saboda haka ba zai yiwu mu isa ga tabbatacciyar natija ba daga abubuwan da suka zo a cikin wadannan littattafaiba.

 


[1] Suratu yusuf, aya ta 4

[2] Suratu yusuf, aya ta 101

[3] Suratu yusuf, aya ta 101

[4] Littafin biharul anwar, wallafar allama majlisiy, juzu’I na 16, shafi na 371

[5] Suratus saffat, aya ta 105, da suratul fathi, aya ta 27.

[6] Littafin alkafiy, na kulayniy, juzu’I na 8, shafi na 91. bugun kamfanin, darul kutub al islamiyya.

[7] Littafin man la yahdhuruhul fakih, juzu’I na 2, shafi na 586

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

  • ina aka samo asalin madogarar gabatuwar jagorancin malami
    8281 Tsare-tsare 2012/07/24
    Mas'alar jagorancin malami a matsayin shugaban al'umma a musulunci wani hakki ne da aka sanya shi ga wanda ya kai matakin ijtihadi. Wasu suna ganin lamari ne sabo a cikin fikirar musulunci, sai dai jagorancin malami a matsayin wani umarni na mai shari'a mai tsarki a lokacin ...
  • shin Imamul hujja a tsibirin bamuda yake zaune?
    14911 تاريخ بزرگان 2012/07/25
    Dalilin da ya sa wasu mutane suka yi ammanar cewa “Tsibirin Bamuda shi ne mazaunar Imamu Mahdi (a.s), gani suke Tsibirin Bamuda shi ne “Jazijrayul Khadra’a”. Bisa kaddara cewa Jaziratuk Khadra’a ita ce mazaunar Imamu Mahdi (a.s) shi ya sa suka ce Tsibirin Bamuda ya kunshi wadannan ...
  • Menene hukunchi namijin da ba ya iya biyawa matarsa hakkokinta?
    12493 2019/06/16
    dawwamar rayuwar aure da karfafarta ya dogara da soyayya da kauna da fuskantar juna da girmama juna. Domin iyali su samu tsayuwa da dawwama Addini Muslunci ya sanya hakkoki ga kowanne dayansu ya kuma ayyana musu wajibai a kansu, duk sa”ilin da aka ce akwai hakkoki to ...
  • menene dalili a kan tabbatar shugabancin malami.
    17279 Hakoki da Hukuncin Shari'a 2012/07/26
    Akwai hanyoyi mabanbanta domin tabbatar da “shugabancin malami” sai dai a nan za mu isu da ambaton dalilai guda biyu na hankali da na ruwaya domin tabbatar da ita. Dalili na hankali: Hankali ya tabbatar da wajabcin samun mutumin da ke ...
  • Shin namiji na da wani fifiko a kan mace ta bangaren halitta?
    7667 Falsafar Musulunci 2017/05/21
    Da namiji da mace sun ginu ne a kan abu guda kuma sun samo asali daga tushe guda da kuma rai guda. Sai dai alakarsu da juna shine kan kai su zuwa ga kamala saboda haka ba wani hanya ma da za a iya kwatantasu a matsayin ...
  • mece ce alakar jagorancin malami da jam'iyyu?
    6470 Tsare-tsare 2012/07/24
    Kungiyoyin siyasa, da ma'anar wasu jam'iyyu masu iri-iri akwai su a cikin kowace al'umma tun zamanin da. A yanzu ana ganin jam'iyyun siyasa a matsayin wani abu na tarayyar mutane da 'yancin zabe ne. bisa wannan asasin ne ya zama dole mu kalli wannan lamari a matsayin ...
  • Menene Hukuncin musulmin da ya kashe kafirin da ba bazimme ba?
    6062 حدود، قصاص و دیات 2017/05/22
    Hukuncin musulumci kan kisa idan na gangan ne kisasi za a yi (Kisasi shi ne kashe wanda ya yi kisan kai) idan kuma ba na gangan ba ne diyya za abiya. Amma kafin a yiwa wanda ya yi kisan kai Kisasi akwai sharaDai da ya zama idan ...
  • mi ake nufi da makamta a ranar lahira?
    14494 Tafsiri 2012/11/21
    Abun nufi da makamta a cikin wannan ayar[i] da sauran ayoyi makamantanta[ii] ba shi ne rashin gani irin na duniya ba {wato mutun ya zamo bai gani da idanuwan da yake dasu} , sai dai abun nufi shi ne mutun da ...
  • Shin Dukkan Hadisan Da Suka Zo Game Da Mas’alar Auren Mutu’a Karbabbu Ne?
    15766 Dirayar Hadisi 2012/07/24
    Aure Mai Tsayayyen Lokaci Sunna ne daga Cikin Sunnonin Musulunci, Wanda Halaccinsa ya zo A Cikin Alkur’ani Mai Girma, Kuma Wannan Sunnar ta Gudana A Lokacin Manzon Allah Mafi Girma (s.a.w) da Lokacin Halifa na Daya, da Wani Sashi na Lokacin Halifa na Biyu, Har Lokacin da ...
  • mene ne dalilin haramcin marenan raguna?
    8146 Hikimar Hakkoki da Hukuncin Shari'a 2012/07/25
    Allah madaukaki mai hikima ne, kuma mai hikima ba ya yin wani aiki da wasa da babu hikima, saboda haka ne duk shi’a suka yi imani da cewa dukkan hukunce-hukunce suna kasancewa bisa maslaha ne, kuam a wasu wuraren an yi nuni da dalilin haramci a wasu ...

Mafi Dubawa