advanced Search
Dubawa
7390
Ranar Isar da Sako: 2020/01/05
Takaitacciyar Tambaya
Wasu daga cikin mala’iku ba su da wani aiki sai bautar Allah da yi masa tasbihi, shin wannan aikin da suke yi suna da zabi a kai yin haka ko kuwa? Kuma idan har ba su da zabi a kan hakan, to shin Allah yana da bukatuwa zuwa wannan ibadar ta su ko kuwa?!
SWALI
Wasu daga cikin mala’iku ba su da wani aiki sai bautar Allah da yi masa tasbihi, shin wannan aikin da suke yi suna da zabi a kai yin haka ko kuwa? Kuma idan har ba su da zabi a kan hakan, to shin Allah yana da bukatuwa zuwa wannan ibadar ta su ko kuwa?!
Amsa a Dunkule

Allah baya amfana da ibadar wani daga cikin bayinsa da komai, ba tare da banbancin cewa bawan ya yi ta ne bisa son ransa ko kuwa.

Sai dai yin ibada bisa zabi na da amfani wajen kara samun kamala da daukaka da shiryuwa a sannu a sannu da kara nutsawa a ci gaban wajen samun kusanci da Allah ta’ala, amma idabar sauran samammu wacce ba ta bisa zabi ba, wanda daga cikin akwai mala’ika, na daga cikin abin da yake dabi’a a gare shi wato aka gina halittar sa a kan haka, wanda matukar yana raye to ibada zai yi kuma su mala’iku suna yin wannan ibadar ne ta hanyar riskar girman Allah Ta’ala, da risker kwarjininsa da tsananin girman matsayinsa, ba wai don Allah yana bukatuwa zuwa gare su ko ibadar su ba.   

Amsa Dalla-dalla

Mala’ika halittar Allah ne shi wanda samuwarsa ke wajen dabi’a, za a iya tabbatar da samuwar sa ta hanyar komawa zuwa nassoshin addini da na wahayi da sallamwa fadin Allah ko kuma ta hanyar yin gwaji a cikin rayuwar manyan bayin Allah Ta’ala (mukhlisai da Annabawa da Waliyai).

Wannan samammen da yake wajen dabi’a ba jiki ba ne ballantana mu yi bayanin kan yadda yake da siffarsa, ku kuma mu iya suranta shi, ballantana ma shi halitta ce da wani lokaci ma yana jirkita kama zuwa siffar mutuum kuma mutuum ya gan shi da siffar dan ’adam, a daidai lokacin da bisa hakika shi ba dan’adam ba ne. kamar yadda Maryam (a.s) ta ga Ruhu,[1] ku kuma ka ga mala’ika ya zo wa mutun a matsayin bako makar yadda ya faru da Ibrahim[2] da Ludu (a.s),[3] kamar dai yadda mala’ika Jibril yake zuwa wajen manzon Allah (s.a.w) da siffar Dahiyatul Kalbi. Amma muna da wani gwargwado na masaniya kan cewa suna da wasu iyakoki da nau’o’i daban-daban, ko da yake wannan yana da alaka da yanayin kirar halittarsu. Don haka zaka ga wasu an wakilta su kan lamarin azabtarwa a duniiya wasu kuma kan lamarin azabtarwa a barzahu wasu kuma an wakilta su kan lamarin azabtarwa a ranar alkiyama. Wasu daga cikinsu aikin su shi ne rubuta ayyukan da mutane suke yi wasu kuma suna rubuta abin da Allah ya hukunta da kuma kaddara, wasu daga cikin su suna gudanar da lamari wasu kuma suna saukar da wahayi, wasunsu suna yi wa zuciya ilhama wasu kuma suna kare muminai kuma suka temaka musu, wasun su su shuwagabanni ne kuma bawa sauran umarni wasu kuma ana shugabantarsu kuma suna bin umarnin na sama da su. Wasu an wakilta su kan arziki, an wakilta wasu kan arziki wasu kuma suna rike da lamarin ruwan sama, wasu mala’ikun daukar rai ne. a cikin su akwai wadanda a ko da yaushe suna cikin yin sujjada, wasu kuma ruku’u, wasu kuma a ko da yaushe suna cikin halin yin tasbihi da tahmidi, wasu kuma suna kusa da ka’aba ko kuma warare masu alfarma, suna tare da muminai maziyarta a cikin dawafinsu da kuma ziyararsu. Wasu sun shagaltu da neman gafara da neman ceto ga muminai da mabiya Ali (a.s), wasu kuma suna ta la’antar kafirai suna tsine musu su da mushrikai da munafikai da masu yi wa bayin Allah (a.s) tsaurin ido, ta yadda ko wane daga cikin su na rike aikin da aka sa shi, kuma ba shi da ikon kan tsallake aikin da ka ba shi kuma duk umarnin da aka ba su suna zartar da shi.

Ba komai ake nufi da ibada ba face bayyanar da bautar bawa a gaban ubangijinsa. Duk abin da zai sa ka kara sanin girma da kwarjinin Allah, zai sa mutun ya kara himma wajen bautar Allah da kuma jin kaskanci a gabansa madaukaki. Wannan jin kaskanci da kasantuwar bawan ga Allah Ta’ala na yin nuni kan samun kalamar da bawa ya yi, saboda haka ibada ba abu ne da amfaninsa yake komawa mai bauta da abin bauta ba, sam ba ma wani abu da amfaninsa yake komawa zuwa ga zatin Allah maitsarki, balllantana ma ya zama dalilin da zai sa Allah ya rika halittar bayi, don haka dalilin da ya sa Allah yake halittarsu bayi yake samar da su, shi ne bayyanar da ikon Allah da kuma yin kyautayin ni’imar samarwa ga halittarsa.

Don haka idan bawa ya zabi ya shagaltu da bautar ubangiji to wannan bautar ta sa zata zama sababin samun tsarikin ruhi a gare shi a matakan bauta da mutuntaka. Kenan wannan tasbihin da tahmadin da girmamamwar suna yi tasirin ne ga shi kansa bawan, kuma ba wani amfanin da ubangiji yake samu daga wannan, haka ma idan ya bai yi ta ba wani abu da zai cutar da ubangii. Ballanatana ma idan bawa ya bar yin bauta shi ne zai cutu ya rasa babban sakamakon da ibada ke kunshe da shi.

A Zahiri wannan shubuhar ta darsu a zukatan wasu daga mala’iko; don haka ne ma a lokacin da Allah ya ce zai sanya halifa a doron kasa: sai suka ce ga mu muna yi maka tasbihi muna tsarkake ka, don me zaka sanya a doron kasa wanda zai yi barna ya zubar da jini a cikinta. Amma Allah Ta'ala yana da masaniya kan dalilin da ya sa ya zabi Adam (a.s) su kuma sun gaza sanin haka. Daga nan sai suka ce mu ba mu da wata masaniya sai abin da ka sanar da mu. Don haka sai suka tabbatar da gazawarsu kuma suka yi wa Adam (a.s) sujjada, [4] . A gefe guda an sallama cewa ibadar da bawa ke yi bisa zabi da Masani ta ta fi wacce take ta dabi’a ta wanda aka tilasta shi kima. Don haka ne ma ta farkon take da tasirin da ta biyun ba ta da shi. Wanna ta farkon mai yinta yana tashi ne daga matakin wanda zai iya (yin ibda) ya haura zuwa matakin na iya, (yin ibada) a aikace, amma shi dayan (na biyun) yana da martaba dauwamammiya ne wacce ba ta sa ya kara martaba da matsayin (matakinsa baya camjawa) kuma idan ya saba ya ki yi zai fadi kasa warwasa.

Imam Ali (a.s) ya siffanta mala’ika kamar haka: “ka halicci mala’iku ka yi musu mazauni a sama wadanda ba sa gajiya ba sa gafala kuma ba sa yin sabo. Ba su zauna a cikin tsatso ba kuma ba a dauke su a cikin wata mahaifa ba, sun fi kowa jin tsoron ka kuma sun fi kowa kusanci da kai kuma sun fi kowa yin biyayya ga umarninka, ba sa yin barci.......... kar kuskure ya shiga cikin hankulansu, jikinsu ba ya gajiya, ba su fito daga wani tsatso ba kuma ba su zauna a cikin wata mahaifa ba, ka halicce su da wani tsari na halitta na daban, kuma ka sanya mazauni a gare su, ka girmama su da makwabtaka da kai, ka amnitar da su kan wahayinka, ka kubutar da su daga aibi, ba don karfinka ba da ba su karfafa ba, ba don tabbatrawar ka ba da ba su tabbata ba, ba don rahamarka ba da ba su yi biyayya ba, kuma ba don kai ba da ba su kasance samammu ba.

Tare da wannan matsayin da suke da shi a wajenka da biyayyar da suke maka da matsayinsu a wajen ka da rashin gafalarsu daga al’amarin ka, da zasu tsinkayi abin da ya buya daga gare su na girmanka da sun rena ayyukansu kuma da sun daukikansu masu zunubi, kuma da sun san cewa lalle ba su bauta maka kamar yadda ya kamata ba, tsarki ya tabbata a gare ka mahalicci abin bauta da ban mamaki yadda kake kyautata jarraba bayinka. [5]

Idan aka sa hankali kan maganar shugaban muminai za a gano abubuwa kamar haka, 1. Sirrin wannan bautar 2. Sirrin da ya sa suka yi tsokaci 3. Da sirrin da ya sa suka sallama, suka yi sujja, haka ma zai bayyana a sarari, cewa ibadar su ta buya a cikun sirrin sanin na riska (ilim shuhudi), da suke da shi ga zatin Allah Ta’ala kuma tsaron su ga Allah Ta’ala ya samo asali ne daga kwarjini da girmansa da suke gani tsarki ya tabbata a gare shi. Duk da cewa wannan ilimin da suke da shi gwargwadon sa na da alaka da yanayin zurin samuwarsu da iyakokin samuwar, kuma ibadar su daidai take da zatin su da kuma iyakokinsu, ba daidai take da zatin Allah madaukakin sarki ba.

Wannan yabon da suka yi wa kansu ya samo a asali ne daga karanci masaniyarsu, amma da yake an yaye musu lamarin kuma Allah Ta’ala ya tabbatar musu da gazawarsu wajen kewayewa da sanin hikimar halittar da yake yi, kuma sun tabbatar da jahilcinsu datakaitawarsu don haka sai suka yi wa Adam sujjada bisa umarnin Allah Ta'ala.

A takaice dai mala’iku ibadar da suke yi ba irin ta dan’adama ba ce wacce yake da zabi kan yi ko bari ba, kuma ibadar su ba ta kasance ma’aunin shar’antawa kamar irin ta mutane ba, don haka ne ma ba ta zama dalilin daukakarsa da kara samun matsayi a wajen Allah Ta'ala  ba. Na’an, idan ya bari ko ya takaita nan da na zai zube ya fadi kasa warwas (matsayinsa zai faxo kasa a wajen Allah Ta'ala).

Don haka ibadarsu ta doru bisa iliminsu da masaniyarsu ga zatin Allah madaukakin sarki da riskarsu ga haibarsa da girmansa ta wannan bangaren, ta daya bangaren kuma suna kallon kaskancinsu da guntuwar rayuwarsu iyakantatta ta daya bangaren   

Idan har son yin bauta ya kasance dabi’a ce da aka dasa a cikin dan’adam, sai dai shi yana da bukatar nusarwa da fuskantarwa, - sabanin mala’ika - haka nan kuma Allah Ta'ala ba shi da wata maslaha kan tilastawa mala’iku kuma ba shi bukatuwa zuwa ibdarsu kuma Allah Ta'ala ya tsayu da kansa kuma shi mahalicci ne mai iko, mai hikima kuma masani.

 

An ciro wannan karatun daga:-

  1. kur’ani mai girma surar Fadiri, aya ta 1, saffati aya ta 164; surar takwar aya 21; surar Sajda aya ta 5, 12; suara An’ami aya ta 62; surar Nahli, aya 2,102; surar Bakara 97, Abasa, 16. Sura Ma’ariji, 4; surar Hijiri, 21; hajji, 22; Nazi;ati, 5; Tahrimi, 6; Zariyati, 4; Mumini, 7. Najami, 26; Anbiya’I, 28, da 103; Bakara, 161, da 33 da 248;. Ali Imrana, 39 da 125-124; Tahrimi, 4. Maryam, 7 da 16-19. Zumari, 73. Mudassiru, 30. Zukhrufi, 77.
  2. Daba-daba’I Muhammad Husain, Almizan, daftari intisharat jami’atul mudarrisin, kum, shafi na 5 -13.
  3. Misbahu Yazdi, muhamad taki mu’arifu Kur’an 1 - 3 darul rahil hakki, buugu na shekar ta 1368, Kum, shafi na 283- 295. 

 


[1]  Surar maryam aya ta 16-19.

[2]  Surar Hudu aya ta 69-77.

[3]  Surar hudu aya ta 81

[4] Surau Bakara aya ta 30 - 33.

[5] almizan j 17 shafi na 89 - 10.

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

  • ina aka samo asalin madogarar gabatuwar jagorancin malami
    8281 Tsare-tsare 2012/07/24
    Mas'alar jagorancin malami a matsayin shugaban al'umma a musulunci wani hakki ne da aka sanya shi ga wanda ya kai matakin ijtihadi. Wasu suna ganin lamari ne sabo a cikin fikirar musulunci, sai dai jagorancin malami a matsayin wani umarni na mai shari'a mai tsarki a lokacin ...
  • shin Imamul hujja a tsibirin bamuda yake zaune?
    14911 تاريخ بزرگان 2012/07/25
    Dalilin da ya sa wasu mutane suka yi ammanar cewa “Tsibirin Bamuda shi ne mazaunar Imamu Mahdi (a.s), gani suke Tsibirin Bamuda shi ne “Jazijrayul Khadra’a”. Bisa kaddara cewa Jaziratuk Khadra’a ita ce mazaunar Imamu Mahdi (a.s) shi ya sa suka ce Tsibirin Bamuda ya kunshi wadannan ...
  • Menene hukunchi namijin da ba ya iya biyawa matarsa hakkokinta?
    12493 2019/06/16
    dawwamar rayuwar aure da karfafarta ya dogara da soyayya da kauna da fuskantar juna da girmama juna. Domin iyali su samu tsayuwa da dawwama Addini Muslunci ya sanya hakkoki ga kowanne dayansu ya kuma ayyana musu wajibai a kansu, duk sa”ilin da aka ce akwai hakkoki to ...
  • menene dalili a kan tabbatar shugabancin malami.
    17279 Hakoki da Hukuncin Shari'a 2012/07/26
    Akwai hanyoyi mabanbanta domin tabbatar da “shugabancin malami” sai dai a nan za mu isu da ambaton dalilai guda biyu na hankali da na ruwaya domin tabbatar da ita. Dalili na hankali: Hankali ya tabbatar da wajabcin samun mutumin da ke ...
  • Shin namiji na da wani fifiko a kan mace ta bangaren halitta?
    7667 Falsafar Musulunci 2017/05/21
    Da namiji da mace sun ginu ne a kan abu guda kuma sun samo asali daga tushe guda da kuma rai guda. Sai dai alakarsu da juna shine kan kai su zuwa ga kamala saboda haka ba wani hanya ma da za a iya kwatantasu a matsayin ...
  • mece ce alakar jagorancin malami da jam'iyyu?
    6470 Tsare-tsare 2012/07/24
    Kungiyoyin siyasa, da ma'anar wasu jam'iyyu masu iri-iri akwai su a cikin kowace al'umma tun zamanin da. A yanzu ana ganin jam'iyyun siyasa a matsayin wani abu na tarayyar mutane da 'yancin zabe ne. bisa wannan asasin ne ya zama dole mu kalli wannan lamari a matsayin ...
  • Menene Hukuncin musulmin da ya kashe kafirin da ba bazimme ba?
    6062 حدود، قصاص و دیات 2017/05/22
    Hukuncin musulumci kan kisa idan na gangan ne kisasi za a yi (Kisasi shi ne kashe wanda ya yi kisan kai) idan kuma ba na gangan ba ne diyya za abiya. Amma kafin a yiwa wanda ya yi kisan kai Kisasi akwai sharaDai da ya zama idan ...
  • mi ake nufi da makamta a ranar lahira?
    14494 Tafsiri 2012/11/21
    Abun nufi da makamta a cikin wannan ayar[i] da sauran ayoyi makamantanta[ii] ba shi ne rashin gani irin na duniya ba {wato mutun ya zamo bai gani da idanuwan da yake dasu} , sai dai abun nufi shi ne mutun da ...
  • Shin Dukkan Hadisan Da Suka Zo Game Da Mas’alar Auren Mutu’a Karbabbu Ne?
    15766 Dirayar Hadisi 2012/07/24
    Aure Mai Tsayayyen Lokaci Sunna ne daga Cikin Sunnonin Musulunci, Wanda Halaccinsa ya zo A Cikin Alkur’ani Mai Girma, Kuma Wannan Sunnar ta Gudana A Lokacin Manzon Allah Mafi Girma (s.a.w) da Lokacin Halifa na Daya, da Wani Sashi na Lokacin Halifa na Biyu, Har Lokacin da ...
  • mene ne dalilin haramcin marenan raguna?
    8146 Hikimar Hakkoki da Hukuncin Shari'a 2012/07/25
    Allah madaukaki mai hikima ne, kuma mai hikima ba ya yin wani aiki da wasa da babu hikima, saboda haka ne duk shi’a suka yi imani da cewa dukkan hukunce-hukunce suna kasancewa bisa maslaha ne, kuam a wasu wuraren an yi nuni da dalilin haramci a wasu ...

Mafi Dubawa