advanced Search
Dubawa
7645
Ranar Isar da Sako: 2011/03/19
Takaitacciyar Tambaya
Ruwayar “Allah yana aiko wa wannan al’umma wanda zai jaddada mata addininta duk shekaru dari” tana da sanadi ingantace ko kuwa?
SWALI
Ruwayar “Allah yana aiko wa wannan al’umma wanda zai jaddada mata addininta duk shekaru dari” tana da sanadi ingantace ko kuwa?
Amsa a Dunkule

Wannan hadisin babu shi a cikin littattafan Shi'a, sai dai cewa wsu daga malamai sun yi nuni da shi. Wannan hadisin an same shi a littattafan ahlussunna ne kawai a littafin sunan Abu Dawud (wanda yake daga manyan littattafan hadisin Sunna) kuma bisa zahiri wasu sun nakalto wannnan daga wannan littafin ne. Shahid mutahhari ya yi magana game da wannan hadisin yana mai cewa: “A addinin musulunci akwai mai kawo gyara, sai dai muna imani da cewa a akidar Shi'a mai kawo gyara shi ne Imam mahdi (a.s) wanda zai kawo gyara duk duniya baki daya. Wannan gyaran na duniya ya shafi kowa da komai kuma ba shi da alaka da wannan bahasin namu. Sai dai akwai wani gyara da shafi fada da bidi’o’in da ake son kawo su a addini wanda ya hau kan dukkan mutane a kowane karni da akan samu mutanen da suke son kawo gyara. Sai dai Allah bai yi wani sharadin cewa duk shekaru dari za a same su ba, ko duk shekaru dari biyu, ko duk shekaru dari biyar, ko duk shekaru dubu, duk babu ko daya a ciki.

Amsa Dalla-dalla

Sanadin Hadisin

Wannan hadisin bai zo a littattafan hadisin Shi'a ba, sai dai wasu daga malaman Shi'a sun yi nuni da shi a maganganunsu. Wannan hadisin ya zo a littattafan hadisin ahlussunna a littafin sunan Abu Dawud, kuma wasu daga cikin malaman Sunna kamar Baihaki ya karbo shi daga Abu Dawud. A littafin Abu Dawud ma ya zo ne a cikin wasu ruwayoyi daga Abuhuraira da ya karbo daga annabi (s.a.w) cewa: “Allah yana aiko wani mutum a duk farkon shekaru dari domin raya addinin musulunci” [1].

Mafi yawan malaman Sunna suna ganin hadisin ruwaya mai ruwayar mutum daya da gani mai inganci, kuma sai suka fara neman samun wadanda wannan hadisin zai dabbaku a kansu[2].

Sanin Ma’anar Hadisin

An yi kalamai game da ma’anar wannan hadisin cewa kowace shekara daya za a samu wani daga malamai ko halifofi ko waliyya da zasu mike don su gyara addini, kuma su kawo sabuwar rayuwa ga addini! Don haka ne sai muka samu cewa sun yi sabani kan cewa wannan mutumin daga wane kalar mutane zaikasance, don haka ne sai aka samu sabani mai tsanani kan ayyana hakikanin wannan mutumin.

Malaman Sunna sun yi sabani sai wasu suka ce daga halifofi ne wannan mutumin yake, wasu kuam suka ce daga sarakuna, wasu kuma suka ce daga malamai fakihai[3], don haka ne ma wannan tunani na Sunna sai ya yi tasiri kan wasu daga shi’awa har suka rika kiran wasu malamai da mujaddadai da suka kawo sunayen kowanne daga cikinsu a kan kowace shekara dari[4]!.

Kamar yadda suka yi sabani kan me ye wannan mutumin zai jadda? Asalin addini? Hukuncin shari’a? akidoji? Ko …?

Sabani na gaba da suka yin shi ne shin wannan mutumin zai bayyana ne a  matsayin mai raya addini a kan kowace shekara dari , ko kuma wannan raya addinin da jaddada shi zai kasance ta hannun malamai ne kan kowace shekara dari? [5].

Idan mun lura da cewa wannan ruwayar ba ta zo a cikin littattafan Shi'a ba, zamu ga wasu ruwayoyin sun kore wannan lamarin ne baki daya, don haka ne ma wannan hadisin bai samu karbuwa ba gun shi’awa.

Daga karshe yana da kyau mu kawo wata magana game da mahangar shaheed mutahhari a takaice game da wannan hadisin yayin da yake fada game da wani lamarin da ya kira “Wani dan Tsokaci game da mas’alar mai raya addini” yana mai shiga bayanin wannan mas’alar da cewa: <<Yayin da nake son yin magana game da mai raya addini>> sai na fada cikin tunanin cewa bari na yi bincike kan wannan lamarin. Duk wani bincike da na yi sai na samu cewa ba mu da wani abu makamancin wannan a shi’anci game da mai jaddada addini, kuma ba mu da tabbacin asalin wannan ruwayar ma. Wannan ya zo daga ma’abota Sunna ne, sai na ga a  littattafansu ma babu wannan ruwayar sai a littafin Abu Dawud kawai da ya kawo hadisi daya kawai kan hakan, wannan ma kuma daga abuhuraira da cewa: انَّ اللَّهَ يَبْعَثُ لِهذِهِ الْامَّةِ عَلى‏ رَأْسِ‏ كُلِ‏ مِائَةٍ مَنْ يُجَدِّدُ لَها دينَها. “Allah zai aiko wanda zai jaddada wa wannan al’umma addininta duk kan shekara dari”.

In ban da Abu Dawud wani bai karbo wannan ruwayar ba. Sai dai yaya Shi'a zasu karbi wannan lamarin?..., wannan ruwaya daga Sunna! Su sun yi tunani game da wannan lamarin, kuma sun yi bincike a kai, cewa manzon Allah (s.a.w) ya ce: Wani mutum zai zo kan kowace shekara dari don ya raya (jaddada) wa al’umma addininta. Kuma in ban da Abu Dawud babu wani wanda ya ruwaito wanann lamari. Wai shin dukkan lamarin addini ake nufi ko kuwa a kan kowane sha’ani na addini mutum daya ne zai zo? Kamar a ce malamin addini daya zai zo sai ya gaya lamarin ilimi, daya kuma daga cikin halifofi ko sarakuna zai zo ya yi gyara kamar a karni na farko umar dan abdul’aziz, a karni na biyu harunar rasheed, da …, a karni na bakwai kuma zuwa yau an zama mazhabobi hudu. Shin kuma a kowace mazhaba dole ne wani mai gyara ya zo, ko kuma duka mazhabobi hudun ne mai gyara zai zo a lokaci daya?

 … sai wannan tunanin ya fado cikin shi’awa, kuma ni na duba littattafai masu yawa, da duban farko muna iya cewa farkon wanda ya kawo wannan fikira cikin shi’awa shi ne Shaikh Baha’I da yake ganin wannan lamari a matsayin wani lamarin gaskiya guda daya, kuma yana mai cewa sanadin hadisin ya yi, har ma yana da wata risala da yake kira “Rijal” yayin da yake kawo labarin rayuwar Kulaini sai yake cewa: Shiekh Kulain yana da girma matukar gaske, kuma malaman Sunna suna ganin sa a matsayin mai jaddada mazhabin Shi'a. sheikh Baha’I malami ne da yake da masaniya game da ra’yoyin malaman Sunna, sai ya so ya ba wa sheikh Kulain wannan a matsayin wata falala da daukaka, don haka sai ya kawo cewa wannan maganar ta wannan hadisin daidai ce don ya yi amfani da wannan ruwayar a matsayin wata dama don ba wa sheikh Kulain falala (tare da cewa yana sanin cewa hadisin bai inganta ba gun mazhabin Shi’a).

… a addinin musulunci akwai maganar mai kawo gyara, sai dai wannan a mahangar Shi'a yana komawa zuwa ga hujja Imam Mahadi dan Hasan Askari (a.s) a matsayin mai kawo gyara a duniya baki daya ne. wannan gyara na baki dayan duniya ba shi da alaka da wannan maganar da ake yi. Kuma gyara na musamman da ya shafi yakar bidi’o’I wani abu da ya hau kan baki dayan mutane bai takaita da wani nau’I nasu ba. Kuma a kowane karni a kan samu wasu mutane masu neman kawo gyara, kuma ubangiji bai yi wani sharadin kowace shekara dari, ko kowace shekara dari biyu, ko kowace shekara dubu ba, babu kowanne daga cikinsu da yake ingantacce[6].

 

 


[1] Sajistani, sulaimnan dan ash’ass (Abu Dawud), sunan Abu Dawud, j 4, s 178, Darul kutubul arabi, bairut, BiTo.

[2] Ibn Kasir, mu’ujizatun nabi, s 378, almaktabatut taufikiyya, biJo, biTo.

[3] Hakim Naishaburi, Muhammad bin Abdullah, almustadrak alas sahihain, (da ta’alikin zahabi), j 4 s 568, h 8593, darul kutubul ilmiyya, bairut, 1411, hK.

[4] Musawi zanjani, sayyid Ibrahim, aka’idul imamiyya isna ashariyya, j 3, s 249, mu’assar a’alami, bairut, 1413 hK.

[5] Mu’ujizatun nabi, s 378, sayyid Ali, tashyidul muraji’at ba tafnidul mukabirat, j 2, s 94, markazul haka’ikul islamiyya, Kum, 1427 h K.

[6] Mutahhari, murtadha, majmu’e asar, j 21, s 247 zuwa 253, da talkhisi, bugun intisharat sadra, Tehran.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa