advanced Search
Dubawa
14143
Ranar Isar da Sako: 2012/06/19
Takaitacciyar Tambaya
Me ake nufi da hadisi rafa’i
SWALI
Ina neman karin bayani game da hadisi rafa’i
Amsa a Dunkule

An rawaito hadisi rafa’i daga manzo (s.a.w) da kamanni biyu, daya ya kunshi shari’a da wajabcinta ko daukakar lamarinta kan mutum kamar na aikin da ke kan kowane baligi cikin mutane, na addinin musulunci, a daya bangaren kuma hadisi rafa’I, girman nauyin shari’a wato takalifin hukunce hukuncen musulunci da ke kan daidaiku.

Hadisin farko an rawaito shi ne daga manzo (s.a.w) ta hannun imam Bakir da imam Ridha (a.s), ya dan saba kadan wajan salonsa da kuma da yawan wasu daga alamomin rafa’i da hadisan da aka ambata cikin litattafan shi’a tsofaffi da na baya, saboda haka aka sa shi daga ingantattun hadisai ko ake la’akarinsu daga hannun Shi’a, abin da ke tare da hadisin farko na gwargwadon cikar yanayinsa kamar : daga abi Abdullah (a.s) ya ce manzo (s.a.w) ya ce “an daukakewa al’umma ta abubuwa tara (9) kuskure da mantuwa (mantuwar aikata kuskuren) da abin da aka tilatasu a kansa, da abin da ba zasu iya ba da abin da suke kokwantonsa da hassada da tunani cikin waswasi kan halittun da ba a gaya musu ainihinta ba” kari kan sharhi cikin ma’anar wannan hadisi da bayanin ma’anarsa akwai bincike mai zurfi wajan malaman usulul fikhi wannan (cikin bincike mafi kyan bayani daga ahalus sunnah) a takaicen takaicewa kan wasu usulai (wajan malaman fikihu) daga na karshen Shi’a imamiyya wajan daidaita ma’anar cewa (da abin da ba su saniba) domin tabbatar da sanin shubuha a cikin hukuncin haramci, hadisi na biyu kuma shi ne wanda ya shahara da hadisi rafa’i (dauke alkalami) shi ne hadisin manzo (s.a.w) da aka rawaito daga manzo (s.a.w) ta bangarori da dama wajan sunna daga imam Ali (a.s) har ma daga Aisha.

Amsa Dalla-dalla

An rawaito hadisi rafa’i daga manzo (s.a.w) da kamanni biyu, daya ya kunshi shari’a da wajabcinta ko daukakar lamarinta kan mutum na daga aikin da ke kan kowane baligi cikin mutane na addinin musulunci, a daya bangaren kuma hadisi rafa’I, girman nauyin shari’a wato takalifin hukunce hukuncen musulunci da ke kan daidaiku.

Hadisin farko an rawaito shi ne daga manzo (s.a.w) ta hannun imam Bakir da imam Ridha (a.s), ya dan saba kadan wajan salonsa da kuma da yawan wasu daga alamomin rafa’i da hadisan da aka ambata cikin litattafan shi’a tsofaffi da na baya, saboda haka aka sa shi daga ingantattun hadisai ko ake la’akarinsu daga hannun Shi’a, abin da ke tare da hadisin farko na gwargwadon cikar yanayinsa kamar : daga abi Abdullah (a.s) ya ce manzo (s.a.w) ya ce “an daukakewa al’umma ta abubuwa tara (9) kuskure da mantuwa (mantuwar aikata kuskueren) da abin da aka tilatasu a kansa, da abin da ba zasu iya ba da abin da suke kokwantonsa da hassada da tunani cikin waswasi kan halittun da ba a gaya musu ainihinta ba”.[1]

An rawaito wasu ruwayoyi cikin wadannan babobi da wasunsu kan dauke nauyi (rafai) da ya tabbata bisa abubuwa hudu, wani bangaren kuma bisa abubuwa shida ba tare da samun wani rashin daidaito a cikin ma’anar wadannan ruwayoyin ba, da zaisa mu dauke su wani abin muhimman tarwa ba, kari bisa warware sharhi da ma’anar wannan hadisi da bayanin ma’anarsa bisa binciken da ya zo mai zurfi daga malaman usulul fikihu, wannan kuwa (cikin bincike mafi kyau da bayanin alamomin da suke gaba ga ahlus sunnah) a takaicen takaicewa kan wasu usulai (wajan malaman fikihu) daga na karshen Shi’a imamiyya wajan daidaita ma’anar cewa (da abin da ba su saniba) domin tabbatar da sanin shubuha a cikin hukuncin haramci,[2].

Farkon abin da ya fada cikin wannan hadisi wannan magana an rawaitota ne cikin matsayin (girman) wadatar zuci, ai zabin da Allah (SW) yayiwa annabin musuluci da budi, amma game da abin da ya kebantu da ma’anar rafai anan akwai yiyuwar abubuwa daban daban, wasu na ganini abin da ya zo a zahirin ruwaya na nuni kan babu makawan ya zama wani abu da ya yi irtibadi da annabci, ma’anar wannan na daga al’amuran shari’a wanda ke hannun mai shar’antawa da kasancewarsa mai shari’a.

Saboda haka ba marfu’in ne abin lura ba, a bin lura shi ne lamarin da Allah (SW) ya sanyawa mutane (takalifin shari’a), wanda ba zai yiwu a dinga kallon zahirin hadisin ba, sai dai idan ana nufin daukakar sha’aninsa musamman wajan hukuncinsa na shari’a, hakanan marfu’in zahirinsa farko ba shi ne abin lura ba, kai har ma hukuncinsa na shari’a.[3]

<Allama majlisy yana cewa: abin nufi dan rafai kan iya daukar ma’anar daukakar sha’aninsa wajan karba ko azaba a kansa yayin da aka saba kuma yana daukar matsayi kamar yadda wasu suka ce daukakar asali yake nufi, tare da tsari ko haramcin taklifi > malaman usulul fikihu sun yi bincike mai zurfi kan wannan hadisi da dukkan salo irin salon da ya zo da shi cikin babin bara’a, mafi yawan zancen da ya zo da shi kan ma’anar (rafai) shi ne daukar nauyi kan mutane, wannan kuwa na nuna ba a samu irin wannan dama ba sai kan wannan al’umma, ya ce wannan magana ce marar tushe, wannan dama tun da can akwaita cikin al’umma saboda haka dole ne mu gano ainihin ma’anar (rafai) cikin hadisin? Kuma ya sha’aninsa ya daukaka (rafai) wasu na ganin rafa’insa (daukakarsa)ya game dukkan hukuncin da Allah (SW) ya dora mana, a dabi’an ce idan ka fito da asu daga ruwayoyi kan dalilin hadisin, misali kamar yin kisa kan kuskure da yin sujjadar mantuwa cikin salla domin asalin hukuncin na la’akari kan kuskure da mantuwa hakanan wajan binciken tushe cikin usul magana mai sifar (ba su saniba) ta tseratar da shi domin duk wani hukuncin da bamu sani ba ba za a kama mu da aikata shi ba, idan kuwa ba yana nufin dacewa da ilimi ba (wanda ba na zahirin ma’ana ba) shi ne allama majlisy yake cewa: abin da ake nufi da daukakar sha’ani (rafai) a mafi yawan wurare yana nufin sassauta hukuncin azaba,a wasunsu kuma na nufin dauke tasirin sa, a wani kuma na nufin hani, amma abin takaicewa game da daukewa bisa kuskure da mantuwa a cikin wannan al’umma, babu mamaki don ana kama sauran al’umma dasuka gabata a kansu.

Idan kuwa sauran a’ummun ba a kamasu a kansu wato idan sun yi kuskure ko mantuwa, wannan baya kore tarayyar mu dasu a ciki, amma abin da ake tilasta musu a kansa babu mamaki yana jaza musu jure wahala mai tsanani cikin abin da aka tilastasu akansa, ta inda kuma wannan al’ummar Allah (SW) ya yalwata mata game da irin wanna juriya da yalwatawarsa ta takiyya, amma kan abin da ba su saniba ya dauke musu abubuwa da yawa daga cikinta (ba a bukatar ta) ta yin aiki da tufafin da suke na kwace, da kaya mai najasa da sujjada kan waje mai najasa, jahiltar hukunci cikin mafi yawan mas’alolinda jahiltar hukuncin abubuwan da ba su zo mana ba babu mamaki sauran al’ummun ana kamasu tare da yi musu hukunci da sakewa da magana koda bayan shekara ne, sai dai wannan ya kebantu da wasu daga kebantattun marawaita …[4].

Hadisi na biyu wanda ya shahara da (hadisin rafai), hadisin dauke aikalami shi ne hadisin da aka rawaito cikin da yawa daga daga litattafan ahlus sunna ta hannun imam Ali (a.s), hakanan ma ta hannun aisha, kuma an kara rawaito shi a lokacin khalifa na biyu yayin da zai yi wa wata mahaukaciya da ta aikata laifi haddi, sai imam Ali (a.s) ya mike ya tunatar da halifa nassin hadisi daga manzo (s.a.w) cewa: “an dauke alkalami kan mutane uku, karamin yaro har sai ya balaga, mahaukaci har sai ya yi hankali da kuma mai bacci har sai ya tashi”.[5]

 


[1] Kulainy, alkafy bolume 2 page 463; seikh saduuk, attauhid page 353, alkhisal bolume 2 page 417; majlisy, Muhammad Bakir, bihar bolume 2 page 280; muassasatul wafa’a, Beirut, 1404.

[2] Raji’ul bara’ah

[3] Almuntazary, Husain ali nihayatul usul, bolume 1&2, page 583-584, Kum bugun farko 1415,

[4] Yura’ji’u Biharul anwar bolume 5 page 304.

[5] seikh saduuk, alkhisal bolume 2 page 93-94; aliyyu akbar gafary, Kum 1362; wasa’ilyush shi’a bolume 28 page 24,mu’assasatu Ahlul-bait (a.s) Kum 1409, Bihar bolume 30 page 681.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa